Rwanda ta zargi Congo da kai farmaki

Image caption Rwanda da Congo na musayar yawu kan harin rokoki

Gwamnatin Rwanda ta zargi Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da tsallako mata kan iyaka tare da kaiwa 'yan kasar hari.

Wannan zargi dai ya biyo bayan kashe wata mata 'yar Rwanda da kuma jikkata danta dan kimanin watanni biyu da haihuwa, bayan da wata roka ta sauka kusa da kan iyakar kasar.

Rwanda dai ta zargi sojin Congo da harba makaman artileri da kuma rokoki.

Amma gwamnatin Congo a Kinshasa ta musanta harba rokokin sannan ta zargi 'yan tawayen M23.

Mataimakin wakilin din-din-din na Rwanda a Majalisar Dinkin Duniya, Olivier Nduhungirehe ya ce kasar sa ba za ta bari a cigaba da kai hari a kan iyakarta ba.

Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo na zargin 'yan tawayen M23 kan harba makaman; ta na cewa ya bawa Rwanda cikakkiyar damar farma Congo.

Majalisar Dinkin Duniya na goyon bayan Kinshasa kan wannan batu; ta na amannar cewa makaman da aka harba na tahowa ne daga 'yan Tawayen M23.

Karin bayani