'Yan majalisar kasa sun goyi bayan na Taraba

Gwamnan jihar Taraba Danbaba Suntai
Image caption Komawar Suntai gida ta janyo cece-kecen siyasa a jihar

Wasu 'yan majalisar dokokin Najeriya da suka fito daga jihar Taraba, sun goyi bayan takwarorinsu na jihar, game da matakin da suka dauka a kan batun gwamna Danbaba Suntai.

'Yan majalisar da suka sanya hannu a wannan matsayi sun hada da Sanata Abubakar Tutare da Jerry Manwe da Aminu Ibrahim da kuma Ibrahim Tukur El-Sudi.

A wani taron manema labarai da suka gudanar dazu a Abuja, 'yan majalisar sun kuma zargi wadansu mutane da ke da kusanci da gwamna Danbaba Suntai da kokarin kawo hargitsi a jihar.

A ranar Alhamis ne majalisar dokokin jihar Taraba ta umarci gwamna Danbaba Danfulani Suntai, ya je ya ci gaba da jinya, kana mukaddashin gwamnan ya ci gaba da jan ragamar ikon jihar.