Kotu ta kori bukatar tisa keyar Kone

Image caption Kotu ta hana tus akeyar Justine Kone Katinan

Wata kotu a Ghana ta kori bukatar da Ivory Coast ta gabatar a gabanta dan tisa keyar wani babban abokin tsohon shugaba, Laurent Gbagbo wanda kasar sa ke bukatar sa kan zarge-zargen da ake masa na wawure kudaden kasar.

Alkalin kotun ya ce, zarge-zargen da ake yiwa Justine Kone Katinan sun shafi siyasa.

An kama Mr.Katinan wanda tsohon ministan kasafin kudi ne a Ivory Coast, a Ghana a shekarar da ta gabata.

An dai hambarar da gwamnatin Lauren Gbagbo ne shekaru biyu da suka gabata tare da taimakon sojojin kasa da kasa bayan rikicin da ya biyo bayan kin amincewar da ya yi na faduwa a zaben shekarar 2010.

Yanzu haka dai ya na kotun hukunta manyan laifuka da ke Hague inda ake zarginsa da aikata laifukan cin zarafin jama'a.

Karin bayani