Ba a sallamo Mandela daga asibiti ba

Tsohon shugaban ksar Afurka ta kudu Nelson Mandela
Image caption Mr Mandela ya dade ya an fama da rashin lafiya.

Gwamnatin Africa ta kudu ta musanta rahotannin da ke cewa an sallamo tsohon shugaban kasar Nelson Mandela daga asibiti.

Wanda ya ke cikin mawuyacin hali na rai-kwakwai-mutu-kwa-kwai, tun watan Yuni wannan shekarar.

Sanarwar da gwamnatin Africa ta kudu ta fitar, ta ce Mr Mandela bai koma gidansa dake Johennesburg ba, sanarwar ta ce har yanzu Mr Mandela na asibiti a Pretoria cikin mawuyacin hali.

Al'umar Africa ta kudu da ma duniya baki daya sun nuna damuwa game da dadewar da Mr Mandela ya yi a asibiti.

Shi dai Mr Mandela dan shekaru casa'in da biyar a duniya, shi ne shugaba bakin fata na farko a Africa ta kudu, wanda mutane da dama ke masa kallon Uban kasa.