Magoya bayan Morsi sun fantsama a tituna

Image caption Magoya bayan Morsi na yin sabuwar zanga-zanga

Magoya bayan hambararren Shugaban Masar, Mohammed Morsi sun kwarara kan titunan birane a ko'ina cikin Masar a zanga zangarsu mafi girma a cikin makonni biyu tun bayan da jami'an tsaro suka kashe daruruwan mutane.

Mutane shida sun rasa rayukansu yayin zanga-zangar, inda da dama kuma suka samu raunuka.

An dai tsaurara matakan tsaro domin toshe yankuna a Alkahira da sauran wuraren da ake sa ran za su zagaya.

Gwamnatin da ke samun goyon bayan soji ta kame galibin shugabannin kungiyar yan uwa musulmi -- na baya baya daga cikinsu shi ne Mohammed Beltagi, wanda aka tsare a ranar Alhamis.

Karin bayani