PDP: Gwamnoni 7 da Atiku sun ɓalle

  • 31 Agusta 2013

Rahotanni daga Najeriya na cewa, wasu gwamnoni bakwai na jam'iyyar PDP mai mulki da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar sun ɓalle, yayin da ake ci gaba da taron musamman na jam'iyyar a Abuja.

Wadanda suka balle din sun ce, sun kafa sabuwar jam'iyyar PDP inda suka nada Kawu Baraje a matsayin shugabanta.

Sun kuma ce, sun balle daga PDP saboda jam'iyyar ta kauce daga manufofin da aka kafa ta tun asali.

Gwamnonin da suka ɓalle sun haɗa da na jihohin, Kano, Sokoto, Rivers, Jigawa, Kwara, Adamawa, da kuma Niger.

Dama dai an jima ana takun saƙa tsakanin wasu daga cikin gwamnonin da suka ɓalle da kuma shugabancin jam'iyyar PDP karkashin, Bamanga Tukur.