Putin ya ce akwai shakku a zargin Amurka kan Syria

Shugaba Putin na Rasha
Image caption Shugaba Putin na Rasha

Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya ce, zargin da Amurka take yi cewa, gwamnatin Syria ta yi amfani da makamai masu guba a wajen birnin Damascus ya sabawa hankali.

Shugaba Putin ya kuma ce, idan har Amurka tana da wata kwakkwarar hujja a kan batun hari da makamai masu guban to ta gabatar da hujjar a gaban kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya.

Ya kara da cewa yayi farin ciki da majalidar dokokin Birtaniya ta ki amincewa kasar ta bi sahun Amurka wajen kai hari a Syriar.

Masu binciken makamai masu guba na majalisar dinkin duniya da suka gudanar da binciken zargin amfani da makamai masu guba a wajen birnin Damascus, sun bar kasar ta Syria.

Karin bayani