'Isra'ila ta sa hannu kan yarjejeniyar nukiliya'

Shugaba Hassan Rouhani na Iran
Image caption Ministan harkokin wajen Iran da Sakataten wajen Amurka John Kery za su gana domin tataunawa shirin nukiliyar Iran

Sabon shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce kamata ya yi Isra'ila ta shiga cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, domin raba yankin Gabas ta tsakiya da makaman.

Shugaban ya ce bai kamata a ce wata kasa ta mallaki makaman nukiliya ba.

Ya ce, Iran za ta tsaya kai da fata domin ganin an kawar da makaman nukiliya daga doron kasa, ba tare da bata lokaci ba.

Furucinsa na zuwa ne 'yan sa'o'i kadan gabanin fara wata tattaunawa ta manyan jami'ai tsakanin Iran da Amurka kan shirin nukiliyar Iran dake janyo kace-nace, cikin shekaru shida.