Dubban mata a India na mutuwa kan sadaki

Image caption Mata suna fama da matsaloli iri iri a Indiya

Wasu alƙaluma da hukumar binciken manyan laifuka ta India ta fitar na nuna cewa, mace guda na mutuwa a kasar cikin kowanne awa guda saboda batun da ya shafi sadaki.

Hukumar tace, cikin shekara ta 2012 fiye da mata dubu takwas ne aka kashe akan rikicin da ya shafi sadaki, kuma yawan mutuwar yana karuwa.

A al'adar kasar India dai iyayen amarya ne suke biyan sadaki idan ta yi aure.

Amma mata da dama ne ake kashewa, wasu kuma suke kashe kansu, idan bayan an samu lalle iyayen ango suka matsawa iyayen amaryar domin su ba su sadaki mai tsoka.