An tattara shaida don bincike a Syria

Image caption Ana tattara bayanan gano makamai masu guba a Syria

Masu gudanar da bincike a kan zargin amfani da makamai masu guba a Syria na Majalisar Dinkin Duniya sun ce za su kai tsawon makonni uku suna nazari akan shaidar da suka tattara.

Daga cikin shaidar da suka tattara sun hada da kasa da jini da gashin wadanda harin ya rutsa da su; kuma za su kai dakin gwaje-gwaje dan gwadawa kafin su gabatar da rahoton su ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya.

Masu binciken sun bar Syria a jiya Asabar bayan sun kai ziyara wurin da ake zargin an kai hari da makamai masu guba a kusa da Damascus.

Amurka ta ce fiye da mutane dubu daya da dari hudu ne suka rasa rayukansu bayan da acewarta dakarun gwamnatin Syria suka yi amfani makamai masu guba, lamarin da gwamnatin ta musanta.

Karin bayani