Kerry ya ce sun kara samun shaidu a kan Syria

Sakataren Wajen Amurka, John Kerry
Image caption Sakataren Wajen Amurka, John Kerry

Sakataren hulda da kasashen wajen Amurka, John Kerry cikin awa ashirin da huda da suka gabata an samu kwakkwarar shaidar cewa, anyi amfani da gubar nan mai kashe laka, wato Sarin a Syria.

A hira ta talabijin ba kakkautawa da nufin karfafa hujjojin kai wa Syria hari, John Kerry ya ce, shaidun da aka samu daga gashi da jinin wadanda harin gubar ya shafa sun nuna irin gubar da aka yi amfani da ita. John Kerry ya ce, nan da kwanakin dake tafe, suna fatan majalisar dokoki zata fahimci cewa, ba zai yiwu ba a zura ido Bashar Al Assad ya ci gaba da amfani da guba wajen hallaka jama'a.

Dakarun 'yan adawa na Syria sun yi kira ga majalisar dokokin Amurka da ta mara baya ga yunkurin shugaba Obama .

Karin bayani