An sallami Mandela daga asibiti

Image caption Tawagar motocin da suka kai Mandela zuwa gida

An sallami tsohon shugaban Afurka ta kudu, Nelson Mandela daga wani asibitin Pretoria inda yake jinya.

A wata sanarwa fadar shugaban Afurka ta kudun tace, har yanzu Mandela yana cikin wani hali, amma kuma yana samun sauki.

Likitocin dake kula da shi sun ce, zai ci gaba da samun cikakkiyar kulawa yayin da ya koma gidansa dake birnin Johannesburg.

An dai sakewa gidan na sa fasali domin ya rika samun kulawa irin ta masu fama da rashin lafiya mai tsanani.

Mandela, dan shekaru casa'in da biyar, shi ne ya jagoranci kawo karshen mulkin wariya a Afurka ta kudu.

Ya dai kasance ce ne a asibiti tun daga watan Yuni.