Masar ta dakile harin jirgin ruwa

Image caption Masar ta fsukanci hari a mashigar Suez

Hukumomi a Masar sun ce, sun dakile wani hari da aka shirya kaiwa kan wani jirgin ruwa da yake wuce wa ta mashigin ruwa na Suez.

Hukumar da ke kula da mashigin ruwan na Suez, ta ce an shirya kai harin ne kan jirgin ruwan dakon kaya don kawo tarnaki ga zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigin, sai dai harin bai yi wata illa ba.

Hukumar ta ce sojojin Masar sun dauki kwakkwaran mataki kan lamarin.

Sanarwar ba ta yi karin bayani kan harin ba, sai dai wasu da suka shaida lamarin sun ce sun ji kara biyu masu karfi a dai-dai lokacin da jirgin ke wucewa ta mashigin.

Mashigin ruwan na Suez, na da matukar mahimmanci wajen safarar hajoji a cinikin kasashen duniya.

Karin bayani