Obama ya nemi amincewar Majalisa kan Syria

Shugaba Obama ya bukace majalisar dokokin Amurka a hukumance ta amince da daukar matakin Soji akan Syria.

Kudurin dokar yana bukatar amincewa ayi amfani da karfin soji dan hana gwamnatin Syria kai hare-hare da makamai ma su guba.

Mr.Obama dai ya bada wannan sanarwar ta bazata ne a jiya Asabar.

'Yan majalisun dai sun yi marhabun da matakin da Obama ya dauka na neman goyon bayansu.

Karin bayani