Farautar giwaye a Afruka Ta Tsakiya

Wata giwa a Afruka
Image caption Farautar giwaye wata babbar matsala ce a Afruka ta Tsakiya

Ofishin Majalisar dinkin duniya mai kula da Afrika ta tsakiya, ya yi kira ga shugabannin kasashen yankin da su hada kai don yaki da masu farautar giwaye ba bisa ka'ida ba.

Kiran ya biyo bayan rahoton da ofishin ya fitar, inda ya ce yawan giwayen ya ragu ainun a yankin, saboda yadda ake kisansu barkatai, duk da cewa a baya-bayan nan kasashe irinsu Kamaru, sun tashi tsaye wajen kare dabbobin.

Bayanan Hukuma dai sun nuna cewa Chadi ta yi asarar giwaye 80 a cikin dare daya, a cikin watan Maris da ya gabata. A Jumhuriyar Afruka ta Tsakiya kuwa giwaye 26 suka hallaka, sannan kuma Kamaru ta yi asarar giwaye dari ukku daga bara ya zuwa bana.

Karin bayani