Mutane 5,000 sun rasa muhallinsu a Ghana

Ambaliyar ruwa a Ghana
Image caption Ambaliyar ruwa a Ghana

Ruwa kamar da bakin kwarya da aka yi a arewacin Ghana ya janyo ambaliyar ruwa, abin da ya sa mutane 5,000 suka rasa muhallinsu.

Ambaliyar ruwan kuma ta yi sanadiyyar mutuwar wata mace mai ciki.

Kimanin gidaje 700 ne ambaliyar ruwan ta shafa a arewacin Ghana, bayan kwashe kwanaki biyu ana ruwan sama.

Tun da damunan bana ta kankama, kasashen Najeriya da Nijar da Mali da kuma Ghana na daga cikin kasashen yammacin Afrika da suka fuskanci ambaliyar ruwa.