An kama 'yan ci-rani 2,500 a Malaysia

Image caption Wasu mata 'yan ci rani a Malaysia

Mahukunta a Malaysia sun ce sun kama baki 'yan ci-rani dubu biyu da dari biyar a wani mataki da suka fara dauka na tisa keyar baki 'yan ci-rani dubu dari biyar da suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba.

Dubban 'yan sanda da sojoji da jami'an shige da fice ne aka saka a cikin shiri mafi girma na zakulo ma'aikata 'yan kasar waje

Galibin mutanen sun zo ne daga kasashen Indonesia da Bangladesh da kuma Burma.

Jami'ia sun ce suna maida hankali ne kan 'yan ciranin da suka yi rijista a karkashin shirin yin afuwar da aka yi musu amma kuma suka ki kai kansu domin a basu takarddun shaidar zama a kasar.

Karin bayani