Wani ya sace kansa a Enugu

'Yan sandan Najeriya
Image caption Samuel Ani da Ogbu Faith Oluchi sun hada baki saboda kudi

A Najeriya, rundunar 'yan sandan jihar Enugu ta damke wani matashi bisa zargin yin garkuwa da kansa, kuma ya nemi 'yan uwansa su biya kudin fansa a sako shi.

Rundunar 'yan sandan ta kuma cafke wata mata, wadda matashin mai sayar da akwatin gawa, ya yi amfani da lambar asusunta na banki, aka biya wani bangare daga cikin kudin fansar.

Irin wannan lamari dai wani sabon abu ne, a matsalar sace mutane da jami'ai ke kokawar magance wa a kasar.

Sace mutane a yi garkuwa da su domin neman kudin fansa, wani al'amari ne da ya zama ruwan dare, musamman a kudancin Najeriya.