Morsi zai fuskanci shari'a a Masar

Image caption Mohammed Morsi

Mai shigar da kara na gwamnatin Masar ya ce hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi zai fuskanci shari'a bisa zargin tunzura kashe masu zanga-zanga.

Zargin nada nasaba da tashin hankalin da aka yi a kusada fadar Shugaban kasa a Alkahira a watan Disambar bara, inda aka kashe akalla mutane bakwai a rikicin.

Haka nan kuma wasu wakilan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi su 14 za su fuskanci kuliya bisa wannan batun.

Ana tsare da Mista Morsi a wani boyayyen waje tun da aka hambarar dashi a watan Yulin.

Tun da aka hambarar da Morsi a kan mulki, gwamnatin kasar mai samun goyon bayan soji tana diramma magoya bayan Morsi wadanda ke yin kira a maido dashi a kan mulki.

A watan daya gabata, an kashe daruruwan magoya bayan Morsi bayan da jami'an tsaro suka tawarwatsa sansanoninsu a birnin Alkahira.

Karin bayani