Bam ya kashe sojoji tara a Pakistan

Image caption An kaiwa sojoji hari a jerin gwano a Pakistan

Wani bam da aka dasa a gefen titi a pakistan ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji akalla tara.

Jami'an sojojin sun ce harin ya faru ne a lokacin da jerin gwanon motocin sojojin ya zo wucewa ta kusa da wani kauye da ke kusa da garin Miranshah a arewacin Waziristan.

Yankin wanda ke kusa da iyakar Afghanistan matattara ce ta mayakan Taliban da sauran 'yan gwagwarmaya.

Wani hari da ake zargin wani karamin jirgin yaki na Amurka ya kai a garin a ranar Asabar, ya hallaka mutane uku.

Karin bayani