'Hari a Syria zai taimaka wa Al-Qaeda'

Mataimakin Ministan harkokin wajen Syria, Faisal Mekdad
Image caption Mataimakin Ministan harkokin wajen Syria, Faisal Mekdad

Gwamnatin Syria ta yi gargadin cewa duk wani matakin soji da Amurka za ta dauka kan kasar, tamkar bada goyon baya ne ga kungiyar Al-Qaeda da rassanta.

Mataimakin Ministan harkokin waje na Syrian Faisal Mekdad ya shaidawa BBC cewa, gungun mutanen dake dauke da makamai da Amurka ke marawa baya, su ne suka yi amfani da makamai masu guba amma ba gwamnatin Syria ba.

Hakan na zuwa a lokacin da fadar gwamnatin Amurka ke kokarin shawo kan 'yan majalisar dokokinta, a kan bukatar daukar matakan soji a kan Syria, kafin kada kuri'a a kan batun a mako mai zuwa.

Galibin 'yan majalisar sun dawo daga hutun bazara ne, domin halartar wani taro a kan bayanan sirri da ke nuna cewa, gwamnatin Syria ta yi amfani da makami mai guba mai kashe laka na 'sarin'.

Harin dai wanda aka kai a Damascus ya hallaka sama da fararen hula 1400.

Karin bayani