An yanke wa magoya bayan Morsi hukunci

Image caption Hambararren Shugaban Masar, Muhammed Morsi

An yanke wa wasu 'yan kungiyar 'yan Uwa Musulmi a Masar su goma sha daya hukuncin daurin rai da rai a kan kaiwa sojoji hari.

Sannan kuma an yanke wa wasu 'yan kungiyar su arba'in da biyar hukuncin daurin shekaru biyar kowannansu a kan yin fito na fito da sojoji watan Agusta a birnin Suez.

Wannan shi ne hukuncin farko da aka yanke wa 'yan kungiyar 'yan Uwa Musulmi tun da rundunar sojin kasar ta kaddamar da wani kamfe na yaki da 'ya'yanta bayan hambarar da Shugaba Mohammed Morsi.

Tunda farko wata kotu ta bada umarnin rufe wasu tashoshin talabijin hudu ciki harda gidan talabijin na Al Jazeera a Masar, a matsayin wani bangare na yaki da kafafan yada labarai da ke nuna tausayinsu ga kungiyar 'yan Uwa Musulmi.

Karin bayani