Libya: An sace 'yar Al-Senussi

Image caption Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta ICC ita ma tana neman Al-sanussi domin yi masa shara'a.

An sace 'yar tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar Libya Abdallah El-senusi jim kadan bayan ta fita daga wani kurkuku a birnin Tripoli.

Ministan Shara'a na kasar Salah Almarghanu ya ce an sace Anoud Abdallah Al-senussi ne sa'adda 'yan bindiga suka yi wa 'yan sandan da ke raka ta kwanton-bauna bayan an sako ta daga kurkukun Al-rayoumi ranar litinin da rana.

Anoud Sanusi dai ta gama zaman kurkuku na watanni 10 ne saboda shiga Libya da fasfo na bogi a watan Oktoba na shekara ta 2012.

Ana dai tsare da mahaifinta saboda zarginsa da ake da hannu wajen aikata manyan laifuka a lokacin mulkin Ghaddafi.

Karin bayani