ICC: Majalisar dokokin Kenya ta kira zama

Image caption Shugaba Kenyatta da mataimakinsa Ruto suna fuskantar tuhumar kotun duniya

Majalisar dokokin Kenya za ta yi wani zama na gaggawa domin yin mahawara kan yadda kasar zata fita daga zama mamba a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, wato ICC.

Mataimakiyar kakakin majalisar ce ta kira a yi mahawarar ranar Alhamis.

A makon gobe ne mataimakin shugaban kasar ta Kenya, William Ruto, zai bayyana a gaban kotun akan tuhumar take hakkin bil-adama.

Yayin da shi kuma shugaba Uhuru Kenyatta zai bayyana a kotun a watan Nuwamba.

Ana dai zarginsu ne dai laifin da ya shafi rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar na shekara ta 2007.