Yunwa na tafe a Zimbabwe

Image caption Shugaba Robert Mugabe

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutane miliyon biyu a kasar Zimbabwe za su fuskanci yunwa a watannin dake tafe.

Hukumar ta ce mutum daya cikin hudu na al'ummar karkara a kasar na bukatar tallafin abinci wanda ya zarta adadin mutanen da suka bukaci taimakon abinci a shekara ta 2009.

Lamarin ya fi muni a kudancin Zimbabwe inda ba a samu amfanin gona mai kyau ba.

A cewar hukumar an samu karancin abinci ne sakamakon rashin kyawun yanayi da tsadar iri da na takin zamani da kuma na sauran kayayyakin noma.

Karin bayani