An harbe wani jariri a New york

Image caption Mutane dai sun fara zuwa unguwar da lamarin ya faru domin yin ta'aziyya.

'Yan sandan birnin New York na Amurka sun shiga farautar wani dan bindiga, da ya harbe wani jaririn da ke ciki wani keken yara.

An harbi yaron mai shekara daya ne a gefen kansa, a yankin karamar hukumar Brooklyn.

Kwamishinan 'yansanda, Raymond Kelly ya ce ya yi amanna cewa mahaifin yaron aka hara, wanda shi ne ke tura keken jaririn a kan titi, kuma lamarin na da alaka da harkar kungiyoyin 'yan daba.

Magajin garin New York Michael Bloomberg, ya ce kisan wani babban abin fargaba ne ga iyayen yaron, da al'ummar yankin na Brookyn da ma birnin ga baki daya.

Karin bayani