Yajin aiki a Afrika ta Kudu

Image caption Ma'aikatan ma'adinai a Afrika ta Kudu

Ma'aikatan hako zinari a kasar Afrika ta Kudu su 80,000 za su soma yajin aiki don bukatar karin albashi.

Kungiyar ma'aikatan ma'adinai ta kasa-NUM na bukatar a kara albashi da kashi 60 cikin 100.

Ma'aikatan a makon daya gabata sun ki amincewa da karin albashi na kashi 6 cikin 100 kamar yadda hauhawar farashin kayayyaki yake a kasar.

Afrika ta Kudu ce kasar da ta fi kowacce a duniya samar da zinare amma a 'yan shekarunnan tana fuskanatar koma baya.

An kiyasta cewar yajin aikin zai janyo wa Afrika ta Kudu hasarar kusan fan miliyon 20 a kowacce rana.

Kungiyar kwadago ta NUM na kunshe da kashi 64 cikin 100 na ma'aikatan hako zinare su 120,000 a Afrika ta Kudu.

Karin bayani