'Sudan za ta bari a fitar da mai ta cikinta'

Image caption Da alama ganawar da shugabannin biyu za ta kawo sauyi wajen dangantakarsu

Shugaban Sudan, Omar al-Bashir, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta bari Sudan ta kudu ta ci gaba da fitar da mai ta bututan man da suka ratsa ta kasarsa.

Al-Bashir ya bayyana wannan mataki ne a karshen wata ganawa ta kwana guda da ya yi da takwaransa na kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir, yana mai yin alkawarin cewa zai cika alkawuran da kasarsa ta kulla da Sudan ta Kudu, cikinsu har da wadanda suka shafi man fetur.

A baya dai hukumonin Sudan sun yi barazanar dakatar da tura mai daga Sudan ta Kudu ta bututan da suka ratsa ta cikinta zuwa bakin teku inda ake safararsa zuwa kasuwannin kasashen duniya.

Kasashen biyu dai suna yawan rikici a kan kudin da ake samu daga sayar da man har ta kai da dakatar da fitar da shi, lamarin da ya jawo musu asara a fannin tattalin arzikinsu.

Karin bayani