'Yan gudun hijiran Syria sun kai miliyan 2

Wasu 'yan gudun hijiran Syria
Image caption Kimanin mutane dubu biyar ne ke fita daga Syria a kowace rana

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu ta yiwa 'yan gudun hijiran Syria miliyan biyu rijista.

A cikin wata sanarwa da ta fitar daga shalkwatarta da ke birnin Geneva, hukumar ta yi imanin cewa adadin zai kai miliyan uku da rabi nan da karshen wannnan shekara.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan 5 sun yi hijira daga muhallansu na asali, zuwa wasu wurare a cikin kasar ta syria, abin da ke nufin yanzu sulusin al'ummar 'yan gudun hijira ne.

Kasashe hudu da suka hada da Lebanon da Jordan da Turkiya da kuma Iraki ne, ke karbar bakuncin galibin wadannan 'yan gudun hijirar miliyan biyu.

Ana sa ran ministocin harkokin wajen kasashen hudu za su hadu a Geneva ranar Laraba, domin su kara neman taimakon kasashen duniya wajen kula dasu.

Karin bayani