Sarakuna mata na taro a Uganda

Image caption Sarauniyar Ingila, Elizabeth

Sarakuna mata da iyayansu da kuma gimbiyoyi na kasashen Afirka na taro a Kampala, babban birnin kasar Uganda, kan hanyoyin da za a bi wajen kawar da wasu al'adun gargajiya dake illa ga mata.

Taron wanda sarakuna mata biyu na Uganda suka karbi bakwancinsa, zai duba yadda za a karfafa hakkokin mata a nahiyar.

A wajen taron ne kuma za a kaddamar da kungiyar mata na Afirka masu rike da sarautun gargajiya, wanda Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya.

Yanzu haka dai akwai masarautun gargajiya a kasashen Afirka da dama, da suka hada da Ghana da Uganda da kuma Swaziland.