Dangote ya karbo rancen gina matatar mai

Image caption Alhaji Aliko Dangote

Rukunin kamfanonin Dangote a Najeriya ya sanya hannu a kan wata yarjejeniya ta karbo rancen sama da dala biliyan uku don gina wani katafaren kamfani da ya kunshi matatar mai da masana'antar takin zamani.

Rukunin kamfanonin ya ce da zarar an kammala wannan matatar mai, Najeriya za ta daina shigo da tataccen mai daga waje.

A yanzu dai kasar na shigowa ne da akasarin man fetur din da ake da shi daga waje saboda matatun man kasar guda hudu ba sa samar da adadin man da ya kamata su samar.

Shugaban rukunin kamfanonin, Alhaji Aliko Dangote ya ce idan aka kamalla ayyukan, dubban 'yan Najeriya za su samu aikin yi.

Alhaji Aliko Dangote ne mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afrika.

Karin bayani