An rantsar da Shugaban Mali

Image caption Shugaba Ibrahim Boubacar Keita

An rantsar da sabon Shugaban Mali, Ibrahim Boubacar Keita, a babban birnin kasar Bamako.

Nan gaba a cikin wannan watanne, za a yi kasaitaccen biki wanda aka gayyaci Shugaban Faransa, Francois Hollande.

Dakarun Faransa sun taimaka wa gwamnatin Mali ta fatattaki 'yan tawayen azbinawa da masu tsatsaurar ra'ayin Musulunci a farkon wannan watan.

Shugaban riko Dioncounda Traore wanda ya mika wa Mista Keita mulki, ya bayyana irin kalubalen da ya fuskanta musamman kwato yankunan da 'yan tawaye suka kwace.

Wakilin BBC ya ce akwai jan aiki a gaban Mista Keita wajen shawo kan rikici a kasar da kawo zaman lafiya a arewacin Mali da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Karin bayani