'Yan majalisa 57 sun koma 'sabuwar' PDP

Image caption Alhaji Atiku Abubakar jigo ne a bangaren da ya balle

Bisa dukkan alamu rikicin da jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ke fuskanta na kara ruruwa, bayan da wasu 'yan majalisar wakilai su 57 suka nuna goyon bayansu ga bangaren da ya balle.

'Yan majalisar a wata sanarwar da aka baiwa manema labarai, sun nuna mubaya'arsu ga bangaren 'sabuwar' PDP wande Alhaji Kawu Baraje ke shugabanta.

Tsohon mataimakin Shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar da gwamnoni bakwai ne suka balle bisa zargin nuna rashin adalcin da suka ce ana yi a 'tsohuwar' jam'iyyar.

Tuni dai bangaren 'sabuwar' PDP ya kai kara gaban kuliya don hana bangaren shugabancin Alhaji Bamanga Tukur bayyana kansa a matsayin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta PDP.

Wadanda suka ballen dai na bukatar shugaba Goodluck Jonathan ya fasa aniyarsa, ta sake tsayawa takara a shekara ta 2015, tare da sauke shugaban jam'iyyar, Alhaji Bamanga Tukur.

Karin bayani