'Yan 'sabuwar' PDP za su rasa mukamansu

Image caption Alhaji Atiku Abubakar ne ya jagoranci bore

A Najeriya, shugaban jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, Alhaji Bamanga Tukur, ya ce 'ya'yan jam'iyar wadanda suka balle, suka kuma kafa sabuwar jam'iyar PDP, sun yi sojan gona ne.

Ya kuma bukaci 'yan Najeriya, musamman jami'an tsaro, da su rika daukarsu a matsayin wadanda suka yi sojin gona.

Shugaban na jami'yar ta PDP ya kuma yi kira ga wadanda aka zaba a karkashin jam'iyar, amma suka nuna goyon bayansu ga wadanda suka balle, da cewa su sauka daga kan mukamansu.

Sai dai lauyoyi na cewa wadanda suka kafa wani bangare na jam’iyya tsarin mulki bai ce za su rasa mukamansu ba.

Don haka akwai gyara a kan ikirarin da jagoran na jam’iyyar ta PDP ya yi.

Jam'iyar PDPn dai ta dare gida biyu inda wasu gwamnoni da 'yan majalisun tarayya da kuma wasu jiga-jiganta suka kafa abin da suka kira 'sabuwar jam'iyar PDP.

Karin bayani