Barci na sabunta kwayoyin halitta na kwakwalwa

Wasu kwayoyin halitta na kwakwalwa
Image caption Barcin da ake mafarki ko kuma wanda ido ke yawan kifta wa ne, ke janyo karuwar kwayoyin halittar na kwakwalwa

Masana sun yi amanna cewa sun gano wani sabon dalilin da ya sa dan Adam ke bukatar barci, domin yana sabunta wasu kwayoyin halitta na kwakwalwa.

Ko da yake an gano hakan ne a tsakanin beraye, amma binciken zai kai ga gano rawar da barci ke takawa, wajen sabunta wani bangaren kwakwalwa idan ya lalace.

An wallafa aikin masanan na jami'ar Wisconsin ne a mujallar 'Neuroscience.'

Rashin yin barci kuma na janyo akasin hakan, inda kwayoyin halittar kan lalace, a cewar masanan.