'An shiga shafukan batsa a Majalisar Birtaniya'

Image caption Jami'ai basu bayyana shafukan da suka kira na batsa ba.

An yi kokarin shiga shafukan intanet na batsa sau 300,000 daga na'urorin kwamfuta da ke majalisar dokokin Birtaniya a bara.

Kimanin mutane dubu biyar ne ke aiki a majalisar ciki har da 'yan majalisar.

Sai dai wani jami'i ya ce alkaluman ba sa nufin duk wadanda suka ziyarci shafukan, sun yi hakan ne da niyyar kallon batsa, saboda watakila wasu sun bude shafukan ne ba tare da sanin abin da suka kunsa ba.

An dai fitar da alkalumman ne karkashin dokar 'yanci samun bayanai.

Karin bayani