Karuwar zazzabin cizon sauro a Chadi

Image caption Cutar ta addabi kasar Chadi

Ma'aikatan lafiya sun yi kashedi ga karuwar da ake samu ta mutane masu dimbin yawa dake kamuwa da zazzabin cizon sauro a yankin kudu maso gabashin kasar Chadi.

Kungiyar agaji ta Medicins Sans Frontiers ta ce adadin masu fama da zazzabin cizon sauron da aka ba da rahoto a yankin Salamat na mutane dubu da dari biyu, ya haura zuwa dubu goma sha hudu a watan Augusta.

A kan samu karuwar masu dauke da zazzabin sauro a lokacin damuna, amma yadda adadinsu ya karu a yanzu ya saaba ma kowanne lokaci.

Zazzabin cizon sauron dai shine musabbabin mutuwar yara da dama a kasar ta Chadi.

Karin bayani