Kokarin warware rikicin gabashin Congo

'Yan tawayen M23
Image caption 'Yan tawayen M23

Shugabannin kasashen yankin Great Lakes na Afirka, sun bukaci Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da ta koma teburin tattaunawa cikin kwanaki uku, tare da 'yan tawayen kungiyar M23, wadanda ke yankin gabashin kasar.

Shugabannin sun ce wajibi ne a kammala tattaunawar cikin makonni biyu.

A cikin watan Mayun da ya gabata ne dai aka dakatar da tattaunawar, wadda aka fara da nufin cimma wata 'yarjejeniya da za ta kawo karshen fada tsakanin bangarorin 2.

An dai samu karuwar zullumi a kwanan nan a yankin, bayan da Rwanda ta zargi Congo da kai farmaki a cikin kasarta.

Rwanda, wadda ake zargi da marawa 'yan tawayen na M23 baya, ta tura sojojinta zuwa iyakarta da kasar ta Congo.