Ministan cikin gidan Masar ya sha da kyar

Ministan cikin gida na Masar, Mohammed Ibrahim
Image caption Ministan cikin gida na Masar, Mohammed Ibrahim

Ministan cikin gida na Masar ya tsallake rijiya da baya, a wani yunkurin kashe shi a kofar gidansa dake birnin Alkahira.

Jami'an tsaro sun ce an kai wa ministan Mohammed Ibrahim, harin ne ta hanyar dana bam a mota, ko da yake bai ji rauni ba.

Sai dai wasu mutane da dama sun jikkata a harin.

Jami'ai sun ce 'yan sanda sun harbe mutane biyu, da ake zargi da kai harin a birnin Nasr dake makotaka da Alkahira.

Harin na zuwa ne a yayin da gwamnatin dake samun goyon bayan soji, ke cigaba da yunkurin ware kungiyar 'yan uwa musulmi, bayan tumbuke Mohammed Morsi.