Shugaban Najeriya ya fara ziyara a Kenya

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya ziyarci Najeriya watanni biyu da suka wuce

Shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan zai fara ziyarar kwana uku a kasar Kenya a ranar Alhamis, da nufin kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyun.

Ana sa ran shugaban zai halarci wani zama tsakanin 'yan kasuwa masu sha'awar zuba jari daga Najeriya da takwarorinsu na Kenya.

Wasu 'yan Najeriya mazauna Kenya dai na zargin cewa ana musguna musu a kasar, lamarin da ya kai su ga yin zanga-zanga makwanni shida da suka wuce.

Dangantaka ta so ta yi tsami tsakanin kasashen, sakamakon zargin safarar miyagun kwayoyi da kasar Kenya ta yi wa wasu 'yan Najeriya da ke zuwa kasarta.