Zaman gaggawa kan ICC a Majalisar Kenya

Image caption Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta

Majalissar dokokin kasar Kenya za ta fara wata ganawa ta gaggawa domin yin muhawara a kan ko ya kamata kasar ta janye daga Kotun manya manyan laifuffuka ta duniya-ICC.

Muhawarar ta zo kasa da mako guda gabanin a fara shari'ar Mataimakin shugaban kasar ta Kenya a kotun ta duniya, a kan zargin aikata muggan laifuffuka na cin zarafin bil-adama.

Haka nan shima Shugaban kasar ta Kenya, Uhuru Kenyatta zai fuskanci shari'a a kotun a watan Nuwamba.

Dukkaninsu suna fuskantar shari'a ne dangane da tashin hankalin da ya biyo bayan zaben da aka yi takaddama akan sa a shekara ta 2007.

Karin bayani