Majalisar Kenya ta amince da kuduri kan ICC

Image caption 'Yan majalisar dokokin Kenya

'Yan majalisar dokokin Kenya sun amince da kudurin janye wa daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC a wata mahawarar gaggawa da suka yi.

Za a gabatar da kudurin cikin kwanaki talatin masu zuwa, bayan da 'yan majalisar jam'iyyar adawa suka kaurace wa kada kuri'a.

Kotun ICC na tuhumar Shugaba Uhuru Kenyatta da mataimakin Shugaban Kasa, William Ruto da aikata muggan laifuka na cin zarafin bil adama, amma duk su biyun sun musanta.

Za a soma shari'ar Mista Ruto a Hague a mako mai zuwa.

Kotun ICC ta ce za a ci gaba da shari'ar koda Kenya ta janye daga cikinta.

Tuhumar da ake yi wa Mista Kenyatta da Mista Ruto na da nasaba da tashin hankalin daya biyo bayan zaben da aka gudanar a shekara ta 2007 inda mutane fiye da 1,000 suka rasu.

Karin bayani