PDP: Ana cacar baki kan shugabanci

Tutar jam'iyyar PDP
Image caption Tutar jam'iyyar PDP

'Yan majalisar dokokin Najeriya da ke bangaren sabuwar PDP, sun maida martani game da barazanar raba su da mukamansu da bangaren Bamanga Tukur ya yi.

Da dama dai ba su ji dadin kalaman Alhaji Bamangan ba, suna masu cewa jama'a ce ta zabe su, kuma jama'a ce kadai za ta sauke su daga mukamansu.

A ranar Laraba ne bangaren Bamanga, ya yi barazanar raba 'yan majalisun da suka koma PDP da ta balle da mukamansu.

Sai dai masana a fannin shari'a sun ce, a karkashin kundin tsarin mulkin kasar, Alhaji Bamanga ba shi da ikon raba su 'yan majalisar da mukamansu, tun da baraka aka samu a jam'iyyar.