Samsung ya fito da sabon agogonsa

Sabbin wayoyin komai da ruwanka na Samsung
Image caption Samsung na kiran agogon 'fashion Icon' a turance, kuma yana da fuska mai launi

Kamfanin lataroni na Samsung ya kaddamar da agogo komai da ruwanka, wanda ke ankarar da mai shi kuma ana iya sa masa manhajoji.

An jima ana dakon fitowar agogon 'The Galaxy Gear', tun da kamfanin shi ne wanda ya fi kowanne sayar da wayoyin komai da ruwanka a duniya.

Kaddamar da agogon ya sa Samsung ya doke Microsoft da Apple da kuma Google.

Masu sharhi

Sai dai masu sharhi sun yi gargadin cewa, idan aka takaita aikin agogon ga sauran kayayyakin Galaxy na Android, hakan zai rage farin jininsa.

A baya dai Samsung ya ce sayar da agogonsa na raguwa, saboda haka masu zuba jari sun kagu su ga kamfanin ya fito da wani abin da zai yi nasara.

Za dai a fara sayar da agogon ne a ranar 25 ga watan Satumba a bikin bajekolin fasaha na Ifa da za a yi a Berlin.

Samsung ya ce farashin agogon na Galaxy zai kai dala 300, ko da yake bai riga ya bayyana ko nawa zai sayar da shi ba a kasuwannin Turai.