Malamai za su yi yajin aiki a Ingila

Image caption Malaman makarantar za su yi yajin aikin ne saboda matsalar albashi

Kungiyoyin malaman makaranta guda biyu mafi girma a Ingila, na shirin tafiya yajin aikin gama-gari na kwana daya, saboda matsalar albashi da fansho da kuma yawan ayyukan da suke yi.

Sai dai kungiyoyin watau NUT da NASUWT ba su sanar da ranar da za su fara yajin aikin ba, amma sun yi kira da a yi tattaunawa, maimakon babatun da gwamnati ke yi.

Sakataren Ilimi, Michael Gove, ya ce ba su da wani dalili na tafiya yajin aikin.

A ranar daya ga watan Oktoba za a gudanar a yajin aiki a yankunan kasar da suka hada da gabashi da tsakiyar Ingila da Yorkshire da Humberside, sannan za a gudanar da wani yajin aikin a wasu yankunan a ranar 17 ga watan na Oktoba.

Ba za a gudanar da yajin aikin a yankin Wales ba.

Karin bayani