Kotu ta ce mata na iya cin gado a Botswana

Image caption Wasu mata 'yan siyasa a kasar Botswana

Wata kotu a kasar Botswana ta kafa tarihi inda ta tabbatar da 'yancin mata na iya cin gado a karkashin dokokin gargajiya, inda kotun ta yi watsi da al'adar nan wacce ta tanadi cewa maza ne kadai za su iya cin gado a kasar.

Alkalan Kotun daukaka kara dake kasar sun zartar da hukunci a shari'ar da wasu mata 'yan uwan juna hudu suka shigar inda suke kalubalantar wani dan uwansu.

Kotun ta ce al'adar nuna bambamci tsakanin mace da namiji ta sabawa hakkin bil adama da gaskiya da kuma adalci.

A cewar kotun zamani ya janza da za a maida mata saniyar ware musamman a kan abinda ya shafi gado iyaye.

Karin bayani