Ana bukatar karin kudi don tallafawa Syria

Image caption 'Yan gudun hijiran Syria

Majalisar dinkin duniya ta ce tana bukatar karin dala biliyan uku da rabi don magance matsalar 'yan gudun hijirar Syria daga nan zuwa karshen bana.

Shugabar hukumar jin kai ta majalisar, Valerie Amos ta shaidawa BBC cewar ya kamata kasashen dake bada taimako su kara bada tallafi.

Majalisar dinkin duniya ta kiyasta cewar mutane miliyan biyu ne suka gudu daga kasar Syria sannan akwai wasu karin mutane miliyan hudu wadanda suka rasa matsugunansu a cikin kasar Syriar.

A cewarta, tashin hankalin na barazana ga tsaro da kuma zamna lafiyar duniya baki daya saboda kaura da jama'a ke yi sakamakon harin da aka kai da makami mai guba.

Karin bayani