Somalia: Al Shabaab ta ce ita ta kai hari

Mayakan kungiyar 'yan tawaye ta al-Shabab
Image caption A shekarar da ta gabata mayakan kungiyar al-Shabab sun kai hari sau biyu gidan cin abincin da ke Mogadishu

Kungiyar Al Shabaab ta ce, ita ta kai harin bama-bamai na ƙunar bakin wake da ya hallaka mutane goma sha biyar dazu a Mogadishubabban birnin Somalia.

An kai harin ne a wani gidan cin abinci.

'Yan sanda sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya zo a cikin wata mota mai dauke da ababen fashewa a cikinta.

Wasu mutane sha biyar sun jikkata a lokacin harin.

Sanannen gidan cin abincin mai suna 'Kauye' ko 'Village' a turance na kusa da fadar shugaban kasar Somalia ne, wajen da 'yan jarida da jami'an tsaro ke zuwa cin abinci.

Karin bayani