Tony Abbott ya zama Praministan Australia

Tony Abbott, Sabon Praministan Australia
Image caption Tony Abbott, Sabon Praministan Australia

A Australia gamayyar jam'iyyu masu sassaucin ra'ayin rikau sun sami gagarumar nasara a babban zaben da aka gudanar.

A cikin jawabinsa bayan nasarar, shugaban jam'iyyun Tony Abbott, ya gaya wa magoya bayansu cewa, zai kafa sabuwar gwamnati wadda mutane za su yarda da ita, wadda za ta yi aiki da gaske.

Ya ce, zai kafa gwamnatin da ta san cewa jama'a fa zasu lura da irin abubuwan da take yi, ba wai irin kalamanta kawai ba.

Tony Abbott ya ce, nan da shekara guda kasafin kudin kasar zai kyautatu har a sami rara, sannan za a daina ganin jiragen ruwan da ke kwaso 'yan ci-rani daga Asiya.

Shugaban jam'iyyar Labour da ya sha kaye, Kevin Rudd, ya kira mista Abbott don yi masa fatan alheri.

Ya kuma ce zai sauka daga shugabancin jam'iyyar ta Labour.