Ana gudanar da zanga-zanga a kasar Brazil

Zanga-zanga a kasar Brazil
Image caption Zanga-zanga a kasar Brazil

Dubban al'ummar kasar Brazil na gudanar da zanga-zangar kin amincewa da cin hanci da rashawa da kuma rashin kyakkyawan shugabanci.

Hakan na zuwa ne yayinda kasar ke bikin zagayowar ranar samun 'yancin kai.

A Rio de Janeiro, wasu masu zanga-zangar su 200, sun tarwatsa wani fareti da sojoji ke yi inda suka gwabza da 'yan sanda wadanda suka harba musu hayaki mai sa hawaye tare da kama wasu daga cikin su.

An cigaba da gudanar da zanga-zangar da yamma a Rio, inda masu zanga-zangar suka rufe hanyoyi.

An kuma samu taho mu gama a wasu biranen kasar, ciki har da birnin Sao Paulo.

Shugaba Dilma Rousseff ta bukaci da a kawo karshen wannan zanga-zanga, inda ta ce a 'yan shekarun nan kasar ta Brazil ta samu gagarumin ci gaba idan aka kwatanta da shekarun baya.